Friday, April 19, 2019

Macizai Sun Bayyana a cikin ofishin Shugaban Kasa




Macizai Sun Bayyana a cikin ofishin Shugaban Kasar Liberiya George Weah har yajawo shugaban aiki daga gida a maimakon ofishinsa.
Sakataren yada labarai na kasar Smith Toby ya shaidawa BBC cewa a ranar Laraba, an ga bakaken macizai guda biyu a ofishin ma'aikatar harkokin kasashen waje wanda kuma a nan ne ofishin shugaban yake.
An dai gargadi ma'aikatan ofishin da su kauracewa ginin har sai ranar 22 ga watan Afrilu.
Mista Toby ya bayyana cewa ''An yi hakan ne domin tabbatar da cewa an sa magani domin magance kwari da macizai da sauransu.''
Ofishin shugaban kasar ya kasance a ma'aikatar harkokin kasashen waje tun bayan wata gobara da aka yi a fadar shugaban kasar.
Wani shafi na labarai a intanet ya saka wani bidiyo da ke nuna yadda ma'aikata ke kokarin kashe macizan a lokacin da suka bayyana a harabar ofishin.
Mista Toby ya ce ''Ba a kashe macizan ba, amma akwai wani dan karamin rami da suka yi amfani dashi domin ficewa
Ankuma  ga 'yan sanda da jami'an tsaron fadar shugaban kasar na tsaron gidan Mista Weah a babban birnin kasar da ke Monrovia, haka kuma akwai ayarin motoci kirar 'Jeep' da kuma motocin da ke raka shugaban ajiye a gaban gidan.
Mista Toby ya ce an fara saka maganin feshi a ma'aikatar harkokin kasashen waje da ke kasar ne a ranar Jumma'a.
Ya kuma yi karin bayani a kan ginin inda ya ce ''ginin tsohon gini ne, saboda yanayin magudanan ruwan mai yiwuwa ne a samu maciji ya shigo ko kuma wasu abubuwa.''
Ana sa ran shugaban zai koma ofishinsa a ranar Litinin bayan an saka maganin ko da kuwa an kashe macizan ko ba a kashe su ba, inji Mista Toby.

No comments:

Post a Comment