Friday, April 19, 2019

CIKA BAKIN SHUGABA BUHARI AKAN YAN NIGERIA




Ba Zan Baiwa ‘Yan Najeriya Kunya Ba- Buhari

Shugaban kasa Muhammad Buhari, ya tabbatarwa da Bilgate cewar ba zai taba baiwa Al’ummar Nijeriya kunya ba.

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya bayyana haka ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da yayi da mai kudin duniya Bilgate, Attajiri Bilgate, ya kira shugaban kasa Muhammad Buhari, don taya shi murnar sake lashe zabe karo na biyu.

Shugaba Buhari yace al’ummar Nijeriya za su yi alfahari da Gwamnatin sa koda bayan ba ya nan, yace yana mai alfahari da yadda Bilgate yake baiwa al’ummar Nijeriya da ma Afirka baki daya tallafi musamman ta fuskar foliyo da cutar kanjamau.

Billgate, yace yana mai alfahari tare da jin dadin kasancewa da shugaban kasa Muhammad Buhari, ya kuma yi alkawarin ci gaba da baiwa Nijeriya tallafin da ya dace domin ciyar da kasar gaba.

Daga karshe shugaba Buhari ya yabawa Billgate kan yadda yake zuba dukiyar sa ta bangaren ciyar da Nijeriya gaba.

No comments:

Post a Comment